Wikipedia:Neman Adminship
A wannan shafin ƙwararrun masu bada gudunmawa zasu Nemi buƙatar zama Admin a Hausa Wikipedia ko wani da yake ganin cancantan wani zai iya nema masa ta hanyar gabatar da shi nominate. Kafin ku nemi Admin ku tabbata kuna da ƙwarewa da kuma jajircewa, sannan kun fahimci dukkanin ayyukan da Admins suke gudanarwa, musamman Ka'idojin kasancewa da dokoki.
Ga duk wanda ke neman ya kasance Administrator zai sanya buƙatarsa a nan ƙasa, haka kuma wanda ke son gabatar da wani, ya tabbata ya sanar da wanda yake son gabatarwa kuma ya amince masa.
Bayan mai neman ɓukatar ya gabatar da kan shi game da neman zama Administrator a Hausa Wikipedia, ana buƙatar dukkanin editoci masu bada gudunmawa da su zo da tambayoyi, shawarwari, ko jaddada goyon bayansu ko rashin amincewa ga mai neman Admin. Ana buƙatar zance na haƙiƙa tare da misalai a duk sanda zaku bada taku ra'ayin. Ku sani ikon Administrator ba gasa bace, haka kuma ba ado bace, ku zaɓi ƙwararru kuma jajirtattun masu sakai dan su kasance Admins hakan zai bada dama a samu inganci da nagarta a Hausa Wikipedia, tun daga bayanan da ake samarwa har zuwa ga editoci masu bada gudunmawa.
Za'a tattauna har na tsawon mako ɗaya, kafin nan duk wani Admin na dindindin zai iya tattara sakamakon tattaunawar, idan mai nema ya samu rinjaye a goyon baya, shi kenan yayi nasara sai a tabbatar da shi ta hanyar kai linki na tattaunawar gaba wajen Stewards dan su tabbatar da shi, idan kuma ya samu rashin amincewa, sai ya koma ya gyara dukkanin kusakuren da aka nuna masa ko wasu fanni da ake da buƙatar ya koma ya samu kwarewa akan su.
Dan nema wa kanku Admin
- Canza
USERNAMEda ke cikin akwatin dake ƙasa zuwa ainihin username ɗinka, sai ka danna maɓallin da ke jiki. - Ka sabunta shafin da zai kaika, ka bi dukkan ka'idojin da ke a shafin ya yin cike buƙatar neman ku. Idan kun gama sai ku yi save.
- Ku sabunta shafin tare da bada amsoshin ga tambayoyin da ke ciki na masu neman zama Admin. Sai ku yi save.
- Ku yi editing shafin nan, Ku sanya na ku buƙatar a sama (ku sauya USERNAME da ainihin username ɗin ku):
{{Wikipedia:Requests for adminship/USERNAME}}